An bayyana rasuwar Alhaji Bukar Makoda a matsayin babban rashi ga al’umma.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon.Jibril Isma'il Falgore ne ya bayyana haka a cikin sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, inda ya jaddada cewa marigayi Bukar Makoda a matsayinsa na kwararren malami kuma hamshakin dan kasuwa ya gudanar da rayuwa mai ma'ana wacce ta cancanci a yi koyi da ita inda ya shafe mafi yawan lokutansa wajen bayar da agaji da taimakawa,mabukata a cikin Al'umma.
Shugaban majalisar Falgore, ya kara da cewa marigayin dattijon ne a jihar nan kuma mutum ne mai matukar mutuntawa wanda ba za a iya mantawa da shi ba kuma al’ummar jihar Kano za su rika tunawa da shi har abada.
Ya kuma yi addu’a a madadin daukacin ‘yan majalisar dokokin Jihar Kano tare da rokon Allah Subhanahu Wata’ala da ya jikansa yasa yana Jannatul Firdaus su kuma iyalansa baki daya Allah ya basu ikon jure wannan rashi maras misaltuwa.
Alhaji Bukar Makoda ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya kuma ya bar ‘ya’ya da jikoki a cikin ‘ya’yansa shi akwai kwamishinan albarkatun ruwa na jihar nan, Hon.Dr.Gwani Ali Haruna Makoda da sauransu.
Uba Abdullahi
Babban Sakataren Yada Labarai