Barrister Salisu Salisu Umar Shugaban Jam'iyar Y.P.P mai bawa kungiyar jam'iyun Jihar Kano shawara akan harkokin shari'a yace Bai kamata gwamanatin Kano ta dana kantomomi ba.

Barrister yayi kiran manema labarai ne domin Kira ga gwamanati akan Kada ta kakabawa mutanen Kano kantomomi a kananan hukumomi na Jihar.

Yace ba dai dai bane a wayi gari gwamanati tace tayi wasu kantomomi na siyasa wanda zasu ja ragamar local government batare da anyi zabe ba ya sabawa Shari'ar zaben kananan hukumomi da dukkan wata doka ta zabe da ake da ita a kasar nan.

S.S.Umar ya kara da cewa  yin hakan ba daidai bane batare da anyi zabe an mika daga zababbu zuwa zabanbu ba.

Yace wannan Jan hankali ne sukewa gwamanatin daga nan zuwa Kwanaki bakwai akan tayi abin da ya dace domin bawa al'ummar jihar Kano damar zaben abinda suke so.

Wanda ya Kara da cewa idan gwamanatin batayi abida ya dace ba to zasu dauki matakin shari'a domin su tabbtar cewa anyi abinda ya kamata yace a ka'ida ba yadda za'ayi kungiyar IPak ta zura idanu tana kallon anayiwa Dimukuradiya karan tsaya batare da tayi yunkurin dakatarwa ba ko Hana irin wannan abun ba.


Post a Comment

Previous Post Next Post