Sunayen sun hadar da Dan.dan takarar shugaban kasa na NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Mustapha Rabiu Kwankwaso yana cikin sunaye guda uku da aka mika wa majalisar dokokin jihar Kano domin tabbatar da su a matsayin kwamishinonin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Gwamna Yusuf ya mika sunayen sabbin kwamishinonin da yake so ya nada.
Da yake tabbatar da jerin sunayen a zauren majalisar a ranar Talata nan, kakakin majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore ya ce jerin sunayen sun kunshi sunayen mutane hudu da aka kebe domin su zama mambobin majalisar zartarwa ta jihar.
A cewar kakakin, jerin sunayen sun hada da Adamu Aliyu Kibiya da Usman Shehu Aliyu da Abduljabbar Garko da Mustapha Rabiu Kwankwaso, wanda ya kasan ce Da ga tsohon gwamnan kano kuma dan takarar shugaban kasa na sabuwar jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Medialink ta waito cewa Kakakin Majalisar ya kara da cewa za a fara tabbatar da sabbin kwamishinonin ne a farkon mako mai zuwa.