Da yake Karin haske ga manema labarai bayan kammala zaman na yau Talata, mataimakin kakakin majalisar Rt. Hon. Muhammad Bello Butu-Butu ya ce wannan matakin da zauren majalisar ta dauka na daga cikin tubalin Kare martabar masarautun da ma jihar Kano baki daya.
Muhammad Bello Butu-Butu ya kara da ce yanzu zasu Mika wannan doka ga kwamishinan kananan hukumomi domin isar da shi ga Gwamna daga nan kuma dokar zata fara aiki a hukumance.
Medialink ta ruwaito Masarautu masu daraja ta biyun zasu kasance kamar haka: Bunkure da Rano da Kibiya zasu kasance karkashin masarautar Rano, yayin da Karaye da Rogo zasu kasance karkashin masarautar Karaye, sai kuma Ajingi da Albasu zasu zama karkashin masarautar Gaya.
Tags
Majalisa