A Ingila An Daure Wata Mata Saboda Zubar Da Tsohon Ciki.

An yanke wa wata mata ‘yar shekaru 44 hukuncin daurin shekaru sama da biyu a gidan yari a kasar Ingila ranar litinin, bisa samun ta da laifin zubar da ciki kimanin watanni takwas da daukar cikin.
Mai shari'a Edward Pepperall a kotun Stoke-on-Trent Crown ya ce shari'ar "mai ban tausayi" ta bukaci ya daidaita 'yancin haihuwar mace da 'yancin dan tayin, kuma ya ce hukuncin na iya hana wasu wuce gona da iri na wa’adin mako 24 don zubar da ciki.

Pepperall ya ce mahaifiyar za ta iya kaucewa zuwa gidan yari da ta amsa laifinta da wuri, kuma ya yanke mata hukuncin ne duk da cewa ta yi matukar nadama da kuma yadda ‘ya’yanta ciki har da mai bukata ta musamman za su sha wahala ba tare da ita ba.

"Kin yi laifi kuma kin sha wahalar damuwa," in ji Pepperall. "Na kuma yarda cewa kina da shakuwa mai zurfi da yaron da ke cikin ki, kuma kina fama da mafarkai da mafarkin ganin fuskar yaronki da ya mutu."

Matar ta kasance makonni 32 zuwa 34 a lokacin da ta zubar da cikin a watan Mayun 2020 ta hanyar amfani da magungunan da aka yi don niyyar amfani da su cikin makonni 10 na farkon ciki, in ji alkalin.

Matar ta sami kwayoyin ne yayin annobar COVID-19 lokacin da aka sassauta dokar hana aikawa da magungunan zubar da ciki ta hanyar da ake aikawa da wasiku. Matar ta yi karya a lokacin da ta shaida wa hukumar ba da shawara kan juna biyu cewa tana da ciki na makonni bakwai, kuma ta ci gaba da yi wa wasu karya ciki har da 'yan sanda, in ji alkalin.

Bayanai sun nuna cewa matar ta gudanar da bincike a shafukan yanar gizo da dama domin kawo karshen cikin da take shi, ciki har da wanda ya ce, "Ina bukatar zubar da cikin amma na wuce makonni 24," alkalin kotun ya rubuta a hukuncin da ya yanke.

Masu goyon bayan kare hakkin zubar da ciki sun soki hukuncin da cewa ya yi tsauri kuma bai zama dole ba, sun kuma yi kira da a kawo karshen aikata laifin zubar da ciki.

Post a Comment

Previous Post Next Post