Masarautar Zazzau ta hana hawan daba a bikin babbar sallah bana.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mallam Yusuf Abubakar Hayat, sakataren masarautar shi ne wanda ya sanar da wannan matakin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Litinin din da ta gaba ta.


Masarautar ta dauki wannan matakin ne bayan tafiyar da Mai martaba Sarkin Zazzau Alh. Ahmed Nuhu Bamalli ya yi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Sanarwar ta kara da cewa, Sarkin wanda tuni ya taya al'ummar masarautar Zazzau murnar barka da sallah, ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Najeriya su gudanar da addu’o'i don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Akan shafe tsawon kwanaki uku ana hawan dawaka a Masarautar Zazzau duk shekara, a wani É“angaren na bikin babbar sallah.

Post a Comment

Previous Post Next Post