Gwamnatin Abba ta rushe Shatale Talen Kofar Gidan Gwamnatin Kano.

Medialink ta ruwaito Gwamnatin jihar kano a ci gaba da rushe-rushen da tace an gina ba bisa ka’ida ba,  ta rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnan jihar a daren jiya talata.

Sai dai har yanzu babu wani bayani da gwamnatin ta fitar a matsayin dalilin rushe shatale-talen.
Shatale-talen dai shi ne mafi kayatarwa cikin manyan shatale-tale da ake da su a fadin jihar kano.
Ko a baya anga yadda gwamnatin ta dinga rushe shi ana narka masu kudade masu yawa don kawata shi.




Post a Comment

Previous Post Next Post