An Kama Wani Babban Malamin Addini Da Auren Mata 75.

Jami’an Tsaro a jamhuriyar Nijar sun damƙe wani Malamin Musulunci mai suna Gausi Almustapha bisa zargin shi da wuce gona da iri, inda ya auri mata saba’in 75 kamar yadda jaridar Taskar Gizago ta rawaito.

Alfijir Labarai ta rawaito Malamin wanda yake zaune a ƙauyen Tudun Faira a yankin Dogon-Dutse na Jihar Dosso, ya yi ƙaurin suna, inda yake ikirarin cewa shi ne Mahadi, wanda zai zo a ƙarshen duniya.

Haka kuma hukumomin na tsaro sun zarge shi da laifin bautar da mabiyansa, inda yake sanya su aikin noma a manyan gonakinsa. Yana kuma aure ‘ya’yansu ba tare da bin tsarin Shari’ar Musulunci ba ta hanyar noman manyan gonakinsa tare da aura masa ƴaƴansu mata.

A halin da ake ciki dai, malamin yana tsare a gidan maza, inda ake shirin yanke masa hukunci.


Post a Comment

Previous Post Next Post