An shawarci al'ummar Musulmi su fara duban watan Babbar Salla a yau.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya umarci Musulmai a faɗin kasan nan da su fara duban watan Dhul-Hijja na shekrar 1444 ta hijira daga yau Lahadi.

Cikin wata sanarwa da kwamitin duban wata na Sarkin ya fitar mai ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu ya ce Sarkin Musulmin ya bayar da wannan umarni ne a jiya Asabar.

Sanarwar ta ƙara da cewa watan Dhul Hijja na da muhimmanci kamar sauran watannin Musulunci, kuma shi ne na 12 cikin jerin watanni kal, wanda a cikinsa ake yin ibadar aikin Hajji, tare da bikin Salla Babba.

"Muna san sanar da duka Musulmi cewa ranar Lahadi 18 ga watan Yuni ita ce ta yi daidai da 29 ga watan Dhul Ƙa'ada, ita ce kuma ranar da ya kamata a fara neman watan Dhul Hijja cikinta na hijira ta 1444." A cewar sanarwar.

Post a Comment

Previous Post Next Post