Hoton kudaden Nigeria Kenan
Darajar naira ta ƙara yin ƙasa a kasuwar canji da gwamnati ke amfani da ita ta Investors and Exporters (I&E) a ranar Juma'a, yayin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da Gwamnan Babban Banki Godwin Emefiele.
Jaridar Punch a Najeriyar ta ruwaito cewa kasuwar ta tashi a ranar Juma'a ana canzar da dala ɗaya kan naira 471.32.
Rahoton ya ƙara da cewa da farko nairar ta ɗan ragu da kwabo 64, idan aka kwatanta da darajarta ta 469.50 a ranar Alhamis. Sai dai kuma ta ƙara faɗuwa har zuwa 471.32 kan dala ɗaya.
Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan bankin ne nan take cikin wata sanarwa, inda aka umarce shi da ya miƙa ragamar CBN ɗin ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa, Folashodun Adebisi.
Mista Adebisi zai kasance muƙaddashin gwamna har sai an kammala binciken zarge-zarge a kan Emefiele da kuma sauye-sauye a bangaren kuɗi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Tags
Kudi