Ana Zaman Magance Matsaloli Tsakanin Makiyaya Da Manoma

 

Hoton wasu makiyaya kenan da manoma

Bayan wani taro na yini uku a Dutse babban birnin jihar Jigawa wanda masu ruwa da tsaki daga jihar Zinder da Jigawan suka halarta, an tattauna kan matakan magance matsalolin da ke haifar da takaddama tsakanin makiyaya da manoma sakamakon zirga zirgar da makiyayan kan yi da dabbobin su a sassan jihohin biyu.

Alhaji Idris Ya’u Mai Unguwa Jaga, shugaban kungiyar manoman Najeriya reshen jihar Jigawa, wanda ya halarci taron, ya ce akwai bukatar masu ruwa da tsaki su sanya ido sosai domin bibiyar yadda za a rinka aiwatar da kunshin yarjejeniyar domin tabbatar da samun nasara.

Su-ma makiyaya wadanda su kayi maraba da kunshin yarjejeniyar sun sha alwashin wayar da kan mambobinsu game da abin da ta kunsa. Alhaji Adamu Idris Babura, shugaban Miyetti Allah a jihar Jigawa, ya ce nan bada jimawa zasu yi gangami daban daban domin fadakar da makiyaya game da alfanun kiyaye ka’idojin yarjejeniyar domin tabbatar da zaman lafiya da manoma.

Mataimakin gwamnan jihar Jigawa Alhaji Aminu Usman ne ya sanya hannu akan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar Jigawa, yayin da gwamnan Zinder ya rattaba hannu a madadin gwamnatinsa.

Kananan hukumomin Sule-Tankarkar da Maigatari da kuma Birniwa a Jihar Jigawa na kan gaba wajen fuskantar rikicin makiyaya da Manoma a duk shekara kuma sune ke kan iyakar Jigawan da Jihar Zinder dake Jamhuriyar Nijar.

Admin

Sulaiman is a Digital Forensic Specialist, Blogger, Graphic Designer and Social Media Influencer with a passion in digitalization of English content into Hausa.

Post a Comment

Previous Post Next Post