Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan dakatar da albashin ma’aikata sama da dubu 10 da gwamnatinsa ta dauka aiki.
Medialink ta rawaito tsohon gwamnan ya koka ne ta cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar kano, Muhammad Garba ya fitar a ranar Laraba, na sakon barka da babbar Sallah ga al’ummar jihar Kano.
Ganduje ya ce dakatar da biyan albashin ma’aikatan da ya dauka aiki ya haifar da damuwa a zukatan ma’aikatan kano, a lokacin da jama’a ke fadi tashin yadda zasu tsira da rayuwarsu .
Hakazalika ya kuma nuna damuwarsa kan soke karin girma da kuma na matakin albashi da ya yiwa malaman makarantun firamare, da gwamnatin tayi
Tags
Kano