Ajibola Bashiru dai shine kakakin majalisar dattijai a majalisa ta tara da wa’adinta yazo karshe a kwanan nan.
Lamarin ya samo asali ne bayan da sanata Ajibola Bashiru yazo masallacin Idi ya zauna a wajen da aka kebe wa mai girma gwamnan jihar ta Osun, sanata Ademola Adeleke,.
Bayan da gwamna Adeleke ya iso masallacin Idi ne sai kawai aka bukaci sanata Ajibola Bashiru ya tashi daga wajen da aka kebe gwamnan zai zauna yayi Sallah, shi kuma ya ce atafau bai san wannan ba, ba wanda ya isa ya sa ya tashi daga wajen.
Rahotanni sun ce wannan lamarin ya janyo gwamnan da sanatan suka fara cacar baki,kamar dai dama zaman doya da manja ake yi, Inda magoya gwamnan da na sanatan suka kara rura wutar rikicin aka nemi bai wa hammata iska, kafin gwamnan yayi fushi ya fasa Sallah a masallacin, ya ja zugansa ya shige garinsu.