Kungiyar Yaki da Rashin adalci da Bibiya a kan Shugabanci nagari Wato War Against Injustice tace tayi Allah wadai da rushe shatale-talen da akayi na kofar gidan gwamnatin Kano.

Kungiyar tace sunyi wannan rubutun ne domin yin Allah wadai da ruguje shatale-talen da Gwamnatin Jihar Kano ta yi na miliyoyin kudi da Gwamnatin da ta shude ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje tayi.
 Wanda suka ce wannan koma baya ne a ci gaban Kano domin gwamnatin da ta shude ta kashe makudan kudade wajen gyara ta amma wannan gwamnatin ta rusa ta ba tare da wani kwakkwaran dalili na yin hakan ba.

 Wannan matakin ya nuna cewa gwamnati mai ci ba ta damu da asusun gwamnati da za a kashe don gina wani sabon ba duk da rashin isassun kudade na kiwon lafiya, ilimi, da ci gaban al'umma a Kano.

 Muna kira ga gwamnatin jihar Kano da ta nemi gafarar Kano akan wannan aiki mara kyau da take.
Sa hannu
Comr. Umar Ibrahim Umar
Darakta zartarwa na Kungiyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post