Rudurar yan sanda kano ta tabbatar da gini ya danne masu ɗibar 'ganima' a wurin rusau na daula hotel dake Kano.

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cewa gini ya danne wasu matasa a wurin da aka gudanar da rusau kan gine-gine a sassan jihar, inda wasu da dama suka jikkata.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da ragowar gine-ginen da aka rusa a Otal din Daula da kuma Filin Idi suka ruguje, daidai lokacin da wasu mutane suke rububin wawashe dukiya a filayen.
Sanarwar ta kara da cewa "Yayin da kwamishinan ƴan sandan jihar ke jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa ransu da waɗanda suka jikkata, ya yi kira ga iyaye, da shugabannin al’umma da su gargaɗi yaransu da su guji waɗannan wuraren."


Post a Comment

Previous Post Next Post