Yanayin wanda a Makkah zai kasance mai zafi da budewar rana da matsakaicin dare, kuma matsakaicin zafin na digiri 43.6 a ma'aunin celcius kuma mafi ƙarancin ma'aunin celcius 29.6.
Cibiyar hasashen yanayin tace birnin Makkah zai kasance da zafi da budewar rana da tsaka-tsaki da daddare.
Hukumar ta NCM ta yi nuni da cewa, matsakaicin gudun iska zai kasance tsakanin kilomita hudu zuwa 10 a cikin sa'a guda a arewa maso yammacin kasar, wanda zai haifar da guguwa kura, da kuma haifar da raguwar hangen nesa.
Hukumar ta NCM ta kara da cewa, yanayin birnin Madina ana sa ran zai kasance da zafi tare da budewa rana da kuma matsakaicin dare, matsakaicin zafin a lokacin aikin Hajji zai kasance digiri 43 a ma'aunin celcius kuma mafi karancin ma'aunin celcius 29.3.
Inda cibiyar ta sake sanarwarcewa, matsakaicin saurin iskar zai kasance kilomita 12 a cikin sa’a guda, inda yayin da iskar za ta yi aiki a wasu lokuta ta hanyar yamma zuwa arewa maso yamma, wanda zata haifar da guguwa tare da kura, wacce ita kuma zata haifar da raguwar sararin samaniya.
Tags
Hajjin Bana