Gwamnan Jihar Kano ya amince da naɗin Ibrahim Garba Shuaibu A Matsayin Sakataren yaɗa Labarai na mataimakin Gwamna Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Ibrahim ya kammala karatunsa na adabi da turanci a jami’ar Bayero da kenan Kano.
Har zuwa lokacin da aka nada shi wakilin jaridar Thisday ne, kuma shugaban kungiyar ‘yan jaridu na Kano.
Sauran wadanda aka nada a matsayin mukaddashin mataimakin gwamna sun hada da.
Lawan Adamu Miko, babban mataimaki na musamman kan harkokin yarjejeniya Abubakar Tijjani Kura, babban mataimaki na musamman kan harkokin mulki Muhammad Garba Gwarzo, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa Abubakar. Salisu Mijinyawa, mataimaki na musamman, na cikin gida Usman Nura Getso, mai taimaka masa a fannin mulki Hamza Ahmad Telan Mata, mataimaki na musamman a bangaren, daukar hoto.
Kuma dukkan nade-naden za su fara aiki nan take.
Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano ya sakawa hannu.
Tags
Kano