Tallafin man fetur da dalilin da yasa batun ke kaɗa hantar yan Najeriya


Tallafin man fetur ba baƙon abu ba ne a kunnuwan ƴan Najeriya, hasali ma, batun cire shi na daga cikin abubuwan da suka fi kaɗa hantar galibin al’ummar ƙasar a cikin shekarun nan.

Kuma yanzu za a iya cewa magana ta ƙare bayan da shugaba Bola Tinubu ya ayyana da bakinsa cewa ba za a ci gaba da bayar da tallafin ba.

Batun cire tallafin man ya zama tamkar ƙadangaren bakin tulu ga gwamnatocin da suka shuɗe, kuma a yanzu ya fara barazana ga sabuwar gwamnatin da ta kama mulki jiya-jiya.

Yunƙurin cire tallafin mai da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ta yi na ɗaya daga cikin manyan tuntuɓen da ta yi, da ake ganin sun kai ta ƙasa.

Gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ma ta yi yunƙurin cire tallafin, sai dai ta ja da baya sanadiyyar turjiya, inda ta ci gaba da lallaɓawa har zuwa ƙarshen wa'adinta.

Sai dai da alama ta bar sabuwar gwamnatin Bola Tinubu da aka rantsar da alaƙaƙai.

A jawabinsa na farko bayan shan rantsuwar kama mulki, Bola Tinubu ya ce "Tallafin mai ya tafi."

Tun daga wannan furuci da ya yi aka shiga ruɗu, layukan motoci na ƙazancewa a gidajen mai, kuɗin sufuri ya tashi, gidajen mai na sayar da litar mai a farashi daban-daban.

Sannan a ƙarshe ranar Laraba kamfanin man fetur na ƙasar, NNPC ya sanar da ƙarin farashi.

Tuni aka fara kai ruwa rana tsakanin sabuwar gwamnatin da ƙungiyar ƙwadago, wadda ta ce za ta yi fito-na-fito da gwamnatin matuƙar aka cire tallafin na mai.

Mene ne cire tallafin man fetur?

Idan za a yi gwari-gwari - Tallafin man fetur wasu kuɗaɗe ne da gwamnatin tarayya ke cirewa daga cikin aljihunta, waɗanda take amfani da su wurin biyan wani ɓangare na kuɗin da ake kashewa wajen sayowa da shigo da tataccen man fetur daga kasuwannin duniya zuwa Najeriya.

Gwamnatin na yin haka ne domin kada a sayar wa al’ummarta man fetur a kuɗi daidai da ainihin farashin kowace lita, bayan la’akari da ƙudin da aka kashe wajen ɗawainiyar shiga da man daga ƙetare.

Misali – idan farashin sayowa da ɗauko man fetur daga ƙasar Belgium (inda can ne a yanzu Najeriya ke sayo tataccen man fetur) zuwa Najeriya yana kamawa naira 700 ne a kan kowace lita, gwamnatin Najeriya kan biya kimanin naira 495 ke nan a matsayin tallafi domin ganin an sayar da lita ɗaya ta man fetur ɗin ga ƴan Najeriya a kan farashin da bai zarce naira 205 ba.

Hakan na nufin idan kana da mota wadda tankinta ke cin lita 50, a duk lokacin da ka cika ta kan farashin naira 205 kowace lita, za ka biya mai gidan mai naira 10,250, yayin da ita kuma gwamnati za ta biya naira 24,750 a madadinka.

Wannan ne ya sanya yadda al'umma ke sayen man fetur a Najeriya ya zamo daya daga cikin mafiya sauki a duniya.

Domin kuwa a 2022 yayin da farashin litar mai a Najeriya bai wuce naira 220 ba, a kasar Ghana ana sayar da ita ne a kan kwatankwacin naira 544, a Jamhuriyar Nijar kuma naira 580, a Afirka ta kudu kuma 489, yayin da a Brazil ake sayar da litar kan naira 633 - Kamar yadda yake a cikin wani rahoto na Dr. Ahmed Adamu, masani kan lamurran man fetur a Najeriya.


Saboda haka idan za a yi bayani a sauƙaƙe, cire tallafin man fetur na nufin gwamnati ta daina cire ko da sisin kwabo daga cikin aljihunta da sunan biyan masu shigo da man fetur domin sassauta farashinsa ga al'umma.

Me zai faru idan aka cire tallafin man fetur

Abin da zai faru bayan cire tallafin mai shi ne abin da akan ce ‘kasuwa ta yi halinta’.

Hakan na nufin za a rinƙa sayar da litar man fetur daidai da farashin da kasuwa ta sawwaƙe

Ma’ana, idan aka kashe naira 700 wajen shiga da litar man fetur ɗaya zuwa Najeriya daga ƙasar waje, za a sayar wa mutane litar man guda a gidajen mai a naira 700 har da ɗoriya, kasancewar su ma ƴan kasuwa za su ƙara ribarsu.

Wato ke nan za a sayar da ita a ainahin farashinta ba tare da wani tallafi daga gwamnati ba.

Haka nan farashin litar man fetur a Najeriya zai rinƙa sauyawa daidai da tashi ko saukan farashin mai a kasuwannin duniya.

Ita kuma gwamnati ba sai ta ware kuɗaɗe domin bayar da tallafin ba.

Me ya sa wasu ke tsoron cire tallafin man fetur?

Masana na ganin cewa rashin tabbas ne babban abin da ya sanya da dama daga cikin al'ummar Najeriya ke baya-baya da batun cire tallafin man fetur.

Babu wani da zai bugi ƙirjin cewa yana da cikakkiyar masaniyar yadda al'amura za su kasance bayan cire tallafin.

Sai dai abu ɗaya da babu haufi a kansa shi ne cire tallafin man zai haifar da gagarumin tashin farashin kayan masarufi.

Dr Ahmed Adamu na jami'ar Nile University da ke Abuja ya ce "Idan kana sayen ruwan gora a farashin naira 200, bayan cire talkafin farashin ruwan zai iya nunkawa fiye da sau biyu.”

A ɓangare guda kuma kuɗaɗen shiga na al'umma musamman ma'aikatan gwamnati da kamfanonin na nan yadda yake - bai ƙaru ba.

Wannan na daga cikin abubuwan da ke tayar wa mafi yawan al'ummar ƙasar hankali kasancewar tashin farashin man fetur zai haifar da tashin farashin sufuri, kuma hakan zai haifar da tashin farashin kusan komai a ƙasar.

Saboda haka abin da al'umma kawai suke hange shi ne uƙubar da za su iya faɗawa ciki, wadda ba su shirya mata ba.

Kuma ga shi babu wani tanadi a ƙasa da gwamnati ta yi kan yadda za a sawwaƙe wa al'umma raɗaɗin hauhawar farashin.

Wannan ne ma abin da ke haifar da takun-saƙa tsakanin gwamnati da ƙungiyar ƙwadago ta Najeriyar, wadda ta ce ba za ta amince da batun cire tallafin man fetur ba har sai gwamnati ta samar da abubuwan da za su tallafa wa al'umma domin rage wahalhalun da za su shiga idan aka cire tallafin.


Admin

Sulaiman is a Digital Forensic Specialist, Blogger, Graphic Designer and Social Media Influencer with a passion in digitalization of English content into Hausa.

Post a Comment

Previous Post Next Post