'YANBINDIGA DADI sun yi awon gaba da Sarkin kauyen Ketti da ke yankin karamar hukumar Babban Birnin Tarayya wato Abuja Municipal, Mr. Sunday Zakwoyi.
‘Yan bindigar da suka zo da yawa sun isa gidan basaraken kai tsaye ranar Juma'a suka balle kofar gidan basaraken da karfi da yaji inda suka tasa keyarsa da wani hadiminsa mai suna Mr. Markus Gade.
Kafin dai su tafi da basaraken, ‘yan bindigar sun kuma abka wani gidan makwabci dake kusa inda shi ma suka sace shi a daidai lokacin da suke ta harba bindiga.
Da yake tabbatar da aukuwar hakan Hakimin Ketti, Alex Akata, ya ce wannan ta'asar ta faru ne a ranar Juma'ar da ta gabata, bayan da yan ta'addan suka mamaye garin suka kuma raba kansu.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da yan bindigar ke abkawa garin ba, domin ko a makonni ukun da suka gabata ma yan bindigar sun mamaye garin inda suka sace wasu mutane masu yawa kuma har yanzy suna hanunsu
Kokarin da wakilin Muryar Amurka a Abuja ya yi don jin ta bakin rundunar ‘yan sandan birnin ya ci tura, kira da rubutaccen sako da ya aike wa kakakin ‘yan sandan bata maida martani ba ya zuwa lokacin da yake hada wannan rahoto.
Aika aikar ‘yan bindiga a yankunan babban birnin tarayya Abuja dai ba wani sabon abu bane, abu ne da dama ya saba faruwa akai akai.
Akan haka nema mahukuntan birnin a baya suka hada kai da jihohi bakwai da ke makwabtaka da birnin domin gudanar da shirin tsaro na bai daya wato OPERATION G7.
Biyo bayan tabarbarewar tsaro a yankin babban birnin tarayyar ne dai ya sa gwamnatin kasar a karshen shekarar da ta gabata ta kebe zunzurutun kudi har Naira Biliyan biyu da miliyan da dari shida don farfado da tsaron, bayan da su ma mahukuntan birnin a watan Oktoban bara su ka kebe wa kananan hukumomin birnin Naira miliyan dari biyar duk dai don hidimar tsaron.
Sai dai kuma duk da wannan matakai da a farko ake ganin jami'an tsaron na kazar kazar wajen daukawa, aika aikar ‘yan bindigar sai ma abin da yai gaba.