Kamfanin NNPCL ya fasa yin shiru, ya magantu akan cewa ba su da niyyar kara farashin man fetur a kasar nan.

A karshe dai Kamfanin Mai na Najeriya mai suna Nigerian National Petroleum Company Limited ya tofa albarkacin bakinsa dangane da fargabar da ake ta yadawa na yuwuwar tashin farashin man fetur na Premium Motor Spirit, wanda aka fi sani da fetur.
 A wani sako da kamfanin ya fitar da misalin karfe 11:48 na daren ranar Litinin a shafinsa na X (Twitter), kamfanin mai na kasa kuma babban mai shigo da mai a Najeriya, ya ce ba ya da niyyar kara farashin man fetur.
 “Ya ku masu girma abokan ciniki, mu a NNPCL Retail muna daraja ku, kuma ba mu da niyyar kara farashin famfo na PMS a ko'ina.

Post a Comment

Previous Post Next Post