CBN ya sha alwashin farfado da darajar Naira a Kasuwar canji.

Babban Bankin Najeriya CBN ya sha alwashin ɓullo da sabbin matakai don magance faɗuwar darajar naira a kasuwar canjin kuɗi.
Matakin na zuwa ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da Muƙaddashin Gwamnan CBN, Folashodun Shonubi a ranar Litinin.


Da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, Mista Shonubi ya ce Tinubu ya bayyana damuwa kan halin da kuɗin ƙasar ke ciki a kasuwar canji ta duniya, lamarin da ya ce zai yi aiki don magancewa.


“Shugaban Kasa ya damu sosai da abubuwan da ke faruwa a kasuwar canjin, ya nuna damuwa game da rayuwar talaka,” in ji shi.

Ya kuma jaddada cewa nan da ƴan kwanaki masu zuwa za a ga kyakkyawan sauyi game da matakan da aka dauka.

Post a Comment

Previous Post Next Post