Dan Majalisar Rano/Kibiya/Bunkure Na Daga Cikin Wanda ke Amfani da Takardun Bogi

 

Akwai yiwuwar kotu ta kwace kujerar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bunkure da Kibiya Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ta bawa Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya, saboda amfani da takaddun bogi.

Tun bayan zaben da ya gabata aka fara gudanar da shari'o'in zabe na kowane mataki a Najeriya. A satin da ya gabata kotu ta yanke hukunci akan zaben Magiri dake jihar Katsina inda kotu ta dawo mishi da Nasararshi, haka zalika a Kano ma kotu ta kwace kujerar dan Majalisa mai wakiltar Tarauni Muktar Umar, duk da yanzu ya daukaka kara, kotun ta yanke hukuncin kwace kujerar ne, saboda amfani da takaddar Primary na bogi.

A yanzu haka ana kan shari'a da dan Majalisar Tarayya na NNPP mai wakiltar Bunkure da Kibiya Hon. Kabiru Alhassan Rurum, kan laifin amfani da takaddun bogi, wanda ake kyautata zaton kotu zata iya bawa Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya kujerar saboda matsalar amfani da takaddun bogi, wanda kuma tuni an bawa kotu shaidun komi da sauran su.

A yanzu haka cikin Gwamnonin jam'iyyar APC na Arewa, akwai Gwamnan da ake zargin mataimakinshi yayi amfani da takaddun bogi, wanda yanzu haka shari'a ta fara tsami, komi na iya faruwa.

Yawanci a shari'o'in zaben bana, akwai rikice-rikice masu yawa akan amfani da takaddun bogi. Yanzu lokaci ne da za'a fara yanke hukunci akan shari'o'in, zamu dinga kawo muku labarin shari'o'in da za'a dinga yankewa musamman na Arewa.

Haka zalika, akwai kyakkyawan labari da muke tsammani game da shari'ar zaben Gwamnan jihar Taraba.

Credit: ✍️ Comr Abba Sani Pantami 


Post a Comment

Previous Post Next Post