Rasha ta aikewa Burkina Faso da tan 2,5000 na Alkama.

Burkina Faso ta ce ta karɓi tan 25,000 na alkama kyauta daga Rasha. Hakan na zuwa ne yayin da ake ƙara samun yauƙaƙar dankon zumunta tsakanin Moscow da ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin soji.

Burkina Faso - wadda ke fama da matsalolin tsaro, sakamakon ayyukan masu iƙirarin jihadi - ta yanke alaƙa da tsohuwar uwargijiyarta wato Faransa, tare da umartar dakarun Faransa su fice daga ƙasar.

A lokacin wani taro ne da aka gudanar a birnin St Petersburg cikin shekarar da ta gabata, shugaban Rasha Vladimir Putin ya alƙawarta aike wa Burkina Faso da kyautar alkamar.

To sai dai ana ganin kamar ba alkamar kaɗai ce aka yi safararta daga Rashar zuwa Burkina Fason ba. A ranar Laraba wasu rahotonni suka ce an ga dakarun Rasha sun sauka a ƙasar.

Dalilan da sojojin Burkina Fason suka bayar na gudanar da juyin mulki har biyu a ƙasar a shekarar 2022 shi ne rashin magance matsalar mayaƙa masu iƙirarin jihadi, waɗanda rikicinsu ya raba fiye da mutum miliyan biyu da muhallansu.

Kusan shekara guda bayan umartar sojojin Faransa su fice daga ƙasar, ana ganin sojojin ƙasar wadda ke da arzikin ma'adinar na ƙara mayar da hankalinsu zuwa ga Rasha wajen neman tallafi.

Post a Comment

Previous Post Next Post