Majalisar Dokokin jahar Kano ta bukaci gwamnatin jahar kano ta gina hanya da gadar da ta hada kananan hukumomin guda uku

Kananan hukumomin sune Madobi Kura da Garin Malam domin inganta harkokin Noma da kasuwanci da al'muran na yau da kullum na yankin.

Dan Majalisa mai wakiltar karamar Hukumar Madobi Sulaiman Muktar Ishaq ne
ya gabatar da Kudirin wanda ya samu goyon bayan Dan majalisa na Kura da Garin-Malam Zakariyya Alhassan daga bisani kuma sauran 'yan majalisar suka amince da shi.
Zaman Majalisar wanda Shugaban ta Alh. Jibril Ismail Falgore ya jagoranta ya kuma nemi gwamnatin jahar kano ta daga darajar Asibitin Tarauni zuwa babban Asibiti.

Kudirin wanda Dan Majalisa mai wakiltar yankin Alh. Kabiru Dahiru Sule ya gabatar domin bunkasa Kula da lafiyar al'umar yankin da Makwabtansa wanda  ya samu goyon bayan 'yan majalisa in da daga bisa ni majalisar ta amince da kudirin nashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post