Majalisar Dokokin jahar kano ta bukaci gwamnatin jahar kano ta baiwa kananan hukumomin jahar kano 44 damar kashe Naira Miliyan 25 kowacce a tsawon watanni 7 domin sayen kayan abinci don rabawa al’umarsu don rage musu radadin kuncin rayuwa.
Wannan na zuwa ne biyo bayan Kudirin gaggawa da Dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Fagge. Tukur Mohd ya gabatar a zaman Majalisar na yau domin kaiwa al'umma daukin gaggawa akan tsadar kayan masarufi da ake fuskanta.
Mataimakin shugaban Majalisar Mohd Bello Butu-Butu da shugaban masu rinjaye Lawan Hussaini wandanda suka tausayawa al’umma bisa kuncin rayuwa da suke fuskanta , sun bayyana cewa samar da abinci ga al'umma zai tai maka waje kai musu dauki.
Zaman Majalisar wanda Shugaban Majalisar Rt.Hon. Jibril Ismail Falgore ya jagoranta ya bukaci gwamnati ta yi amfani da hukumar kyautata Da'a wato CRC da wasu hanyoyi da za su taimaka wajen kaiwa al'umma tallafin abinci.
Majalisar ta kuma nemi 'yan majalisar wakilai da sanatoci na jahar kano da takwarorinsu na jahohi su yi koyi da wannan mataki domin taimakawa al'ummar kasar nan
Khadija Ishaq Muhammad.