Shugaban Majalisar Dokokin jihar kano Alh. Jibril Ismail Falgore ne ya bayyana haka bayan amincewa da rahoton binciken karshe kudin gwamnati da babban mai binciken kudi na jaha ya aikewa Majalisar na shekarar 2021 wanda Shugaban kwamitin Kula da kashe kudin gwamnati na Majalisar Tukur Mohd kuma Wakilin karamar Hukumar Fagge ya gabatar a zaman Majalisar na yau Litinin.
Shugaban majalisar. Jibril Ismail Falgore ya ce ana ware kudaden ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati domin amfanin
al'umar jahar kano amma ba Don morewar wasu tsiraru ba.
Ya ce Majalisar ba za ta amince wasu ma'aikatu su rika wadaka da kudin gwamnati ba, a don haka ya ce ya zamo wajibi su rika dawo da kudaden da ba su gudanar da aiyukan da aka tsara yi a kasafin kudin su ba zuwa asusun gwamnati.
Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ya kara da cewa gwamnati ta warewa ma'aikatun kudaden da suka kamata su gudanar da aiyukan amma abin takaici sun gaza yin haka a madadin haka sun bige da kashe kudin ba bisa ka'ida ba.
Ya ce Majalisar za ta umarci ma'aikatu da hukumomin gwamnati su dawo da irin wadannan kudaden domin amfani da su a wasu ayyuka kuma kudade da za’ayi amfani da su a wasu aiyukan, ya ba da tabbacin Majalisar na yin aiki tare da Gwannatin Abba Kabir Yusuf domin cimma manufofinta na tabbatar da yin aiki da kudin gwamnati yanda yakamata.
Khadija Ishaq Muhammad