Majalisar Dokokin jahar ta umarci Wakilan Hukumar zabe mai zaman kanta ta jahar kano wato KANSIEC su bakwai su dawo da Naira Milan 41 da Dubu 24 da suka kashe su ba bisa ka'ida ba a shekarar 2019 zuwa asusun gwamnatin jahar kano
Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin jahar kano ta maye gurbin Wakilan da wasu da suka cancanci rike matsayin da suke kai.
Matakin ya biyo bayan rahoton bincike da kwamitin
Majalisar mai Kula da harkokin kudi wanda Dan Majalisar mai wakiltar karamar Hukumar Karaye Ahmad Ibrahim Karaye ya gabatar akan rahoton kashe kudaden gwamnati na shekarar 2019.
Khadija Ishaq Muhammad.