Majalisar dokokin jihar Kano ta kammala taron kwanaki uku da ya gudana a Kaduna.

Majalisar dokokin jihar Kano da ma'aikatar lafiya ta jihar Kano Hadi da cibiyoyin raya kasa sun kammala taron kwanaki uku a Bafra da ke jihar Kaduna a inda suka jaddada aniyar su na samar da dokokin kan tantance lafiyar ma'aurata kafin aure da Kuma samar da cibiyar dakile yaduwar cututtika ta garko a jihar Kano da nufin Kara bunkasa matakan dakile yaduwar cututtika a sassan jihar.
Medialink ta rawaito cewa.

Taron wanda kakakin Majalisar dokokin jihar Kano RT Hon jibrin Ismail Falgore ya jagoranta Wanda Kuma ya samu halartar kwamishinan harkokin lafiya na jihar Kano Dr Abubakar labaran Yusuf da mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kano RT Hon Muhd Bello Butu-Butu-,da Shugaban masu rinjaye Hon lawan Hussain da tsohon Shugaban hukumar Hisba Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa,Hon Musa Ali Kachako Wanda ya gabatar da kudin dokar da sauran cibiyoyi kamar su NCDC da RTSL da FCDO-lafiya, LISDEL da E HEALTH AFRICA SOCIETY FOR FAMILY, da AKTH da UNICEF.

Taron dai yayi waiwaye kan yadda dokokin biyu zasu kasance gami duba su ta mahangar addinin musulunci .

Sakataren yada labarai na Majalisar dokokin jihar Kano kamaluddeen Sani Shawai ta cikin sanarwar da ya hannu tare da mikawa manema labarai ta Kara da cewar kakakin Majalisar dokokin jihar Kano RT Hon jibrin Ismail Falgore ya jinjinawa cibiyoyin raya kasa wajen tallafawa Majalisar shirya taron.

Falgore yayi Kuma amfani da damar wajen godewa kwamishinan harkokin lafiya a jihar Kano Dr Abubakar labaran Yusuf da sauran mahalarta taron.

Falgore yayi nuni da cewar Yan Majalisar dokokin jihar Kano zasu yi abinda ya dace bisa shawarwarin kwararru a fannin dokoki da lafiya don tabbatar da kudurorin zama dokoki a yayin da suka koma Zaman Majalisar.

Post a Comment

Previous Post Next Post