Dan Majalisar Dokoki mai wakiltar karamar Minjibir Alh. Abdulhamid Abdul Minjibir ya gabatar da Kudirin a zaman Majalisar na yau.
Zaman Majalisar wanda Shugaban Majalisar Alh. Jibril Ismail Falgore ya jagoranta ya kuma bukaci gwamnatin jahar kano ta gina hanyar da ta taso daga Danbatta zuwa Masallaci zuwa Diggol zuwa Unguwar Kwalba zuwa Gwanda zuwa kwasabari zuwa Dungu zuwa Sansan zuwa Baro zuwa Tasawar Dukawa zuwa Mirirni dukkaninsu a karamar Hukumar Danbatta.
Bukatar hakan ta biyo bayan gudurin da Dan Majalisar yankin Alh. Murtala Musa Kore ya gabatar na bukatar sake gina hanyar wacce a ka gina ta fiye da shekaru 30 da suka gabata inda lalacewar ta ke kawo nasakasu ga cigaban yankin.
MEDIALINK.