Dan Majalisar mai wakiltar Kura da Garin-Malam Alh. Zakariyya Alhassan Isqak ne ya gabatar da Kudirin bukatar aikin wanda ya samu goyon bayan dukkanin 'yan majalisar.
Ya ce lalacewar Asibitin ta kawo nakasu wajen Kula da lafiyar al'umar yankin.
Medialink ta rawaito cewa, Majalisar ta bukaci gwamnatin jahar kano ta samar da wutar lantarki a Garuruwan Kafi da' Yammedi da Kadata da Kadare da dukkaninsu a karamar Hukumar Karaye.
Da yake gabatar da gudurin Dan Majalisar Dokoki mai wakiltar karamar Karaye Engr. Ahmad Ibrahim Karaye ya ce tsawon lokaci al'ummar yankin ba su da wutar lantarki wadda hakan ya kawo koma baya a harkokin sana'o'in dogaro da kai musamman a tsakanin matasa.
MEDIALINK.