Gwamnan jahar kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya nemi Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da nadin kwamishinoni da Sakataren Hukumar zabe mai zaman kanta ta.

5.3.2024

Gwamnan jahar kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya nemi Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da nadin kwamishinoni da Sakataren Hukumar zabe mai zaman kanta ta jahar kano su Bakwai. 

 Shugaban Majalisar Dokokin jahar kano Alh. Jibril Ismail Falgore ne Karanta wasikar gwamnan a zaman Majalisar na yau. 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce kundin tsarin mulkin kasa ne ya ba shi damar nada mutanen 7 akan matsayin.

Medialink ta rawaito cewa Kwamishinonin sun hada da Engr. Kabir Jibril da Dr. Salisu Mohd Tudun Kaya da Alh. Shehu NA'Allah Kura da Isyaku Ibrahim Kunya da Amina Inuwa Fagge da Garba Ibrahim Tsanyawa da kuma Anas Mohd Mustafa a matsayin sakataren Hukumar ta KANSIEC. 

Majalisar ta baiwa kwamitin Kula da harkokin Hukumar zaben wa'adin kwanaki biyu domin ya tantance su tare da mika rarotonsa ga Majalisar. 
Medialink.

Post a Comment

Previous Post Next Post