Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aikewa Majalisar Dokokin jahar kano sunayen jami'an rikon kananan hukumomi guda 17 a kowacce karamar Hukuma.

5.3.2024
A cikin wasikar gwamnan ya ce nadin na su ya biyu bayan karewar wa'adin shugabanin da aka zaba a ranar 12 ga watan Fabrairu. 

Gwaman ya ce an nada su ne bisa tanadin dokar kananan hukumomi ta jahar Kano.

Wasikar ta nemi a nada su tsawon watanni 3 zuwa lokacin da za gudanar da zaben kananan hukumomi. 

Medialink ta rawaito cewa Zaman Majalisar wanda Shugaban Majalisar Alh. Jibril Ismail Falgore ya jagoranta ya baiwa kwamitocin da aka nada domin tantance shugabanin kananan hukumomin umarnin tantance su tare da mika rahotonsu a ranar Alhamis mai zuwa a zama na musamman da Majalisar za ta yi. 
Medialink.

Post a Comment

Previous Post Next Post