Gyaran Dokar Aiki Da Ritaya ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin jihar Kano.

Majalisar Dokokin jahar kano ta yi karatu na biyu akan Kudirin Gyaran Dokar Fansho da Biyan Gratuity karo na Biyar ta shekarar 2024 da Gyaran Dokar Hukumar Majalisa karo na biyu tare da Gyaran Dokar Hukumar Kula da harkokin Kudi da Bangaren Shari'ah. 

Da yake gabatar da Kudirin gyaran Dokokin uku, Shugaban masu rinjaye na Majalisar. Lawan Hussaini Chediyar Gurasa ya ce gyaran dokokin da manufar mayar da wa'adin aikin gwamnati zuwa shekaru 35 ko shekaru 60 na haihuwa za su baiwa Dubban matasa damar samun aiki tare baiwa ma'aikata masu aikin damar samun cigaba a aikinsu. 
Medialink ta rawaito cewa. Karin haske akan Kudirin dokokin, Dan Majalisa mai wakiltar Minjibir Abdulhamid Abdul da na Ungogo Aminu Sa'adu Ungogo sai na Ajingi Tini Lawan da kuma na Madobi Alh. Sulaiman Muktar Ishaq wadanda suka ce, sun bukaci gwamnatin jahar kano ta biya ma'aikatan da barin aiki ya shafa hakkokinsu na barin aiki. 
K.I.M.

Post a Comment

Previous Post Next Post