Azaman majalisar na yau Alhamis 07 03 2024 wanda Shugaban ta Rt. Hon.Jibiril Isma'il Falgore ya zagoranta dokar wanda akawun majalisar Alh.Bashir Idris Diso yayi mata karatu na uku akan ritayar ma'aikata na Jihar nan na shekaru 35 zuwa shekaru 60 na haihuwa da ya dace ko wanne ma'aikaci ya aje aiki a Kano sabanin dokar da wacce ma'aikaci zaiyi shekaru 65 yana aiki kafin ritaya.
Medialink ta rawaito cewa majalisar ta amince da gyaran dokar ne domin bawa sauran al'umar Kano basu damar samun aiki domin suma su bada tasu gudumawar ta yadda za'a ciyar da Jihar Kano gaba.
Da yake karin bayani ga manaima labarai Shugaban masu rinjaye na majalisar Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala Lawan Hussaini yace babu wata hikima GA wanda ya shekara 35 yana aiki ko ya shekara 60 kuma ka bashi wata shekara 5 bayan ga matasa na nan a jibge basu da aikin yi duk kuwa da cewa sunyi karatu suna da Degree,N.C.E kuma suna neman aikinyi wanda suna da ilimi da jini ajika amma baa Basu dama ba.
Lawan Hussaini yace hakan zai bada damar daukar aiki ga matasa idan wandan nan Dattawan suka matsa ya kuma Kara da cewa da zarar gwamna yasa hannu to ma'aikatan da suka Fara dorawa Daga shekaru 65 zasu aje aiki wanda hakan zai bawa gwamanatin Kano damar daukar sabbin ma'aikata.
K.I.M.