Kasar Saudiyya ta sanar da ranakun Arafat da na Eid Al-Adha na shekara ta 2023.

Majalisar koli ta kasar Saudiyya ta ayyana cewa, Litinin 19 ga watan Yunin na shekarar 2023 ne ranar daya ga watan Zul Hijjah a kalandar Musulunci, bayan an ga jinjirin wata a masarautar.

 Hakan na nufin cewa ranar Arafat zata kasan ce ne ranar Talata 27 ga watan Yuni, 2023 yayin da Laraba 28 ga watan Yuni za ta kasance ranar Idin Al-Adha.

 Kamfanin dillancin labaran iqna ya rawaito cewa, anga jinjirin watan ne daga shafin sadarwa na yanar na SPA cewa, an ga watan Dhul Al Hijjah wanda shi ne na karshe kuma na 12 ga watan na kalandar musulunci a birnin Tumair na kasar Saudiyya a jiya Lahadi.

 A baya Saudiyya ta yi kira ga Musulman kasar da su fara duban jinjirin watan da zai iya nuna ranar bikin Eid Al Adha na 2023.

 Majalisar koli ta Masarautar ta ce duk mutumin da ya ga jinjirin watan, ko dai da abin rufe fuska ko kuma ido da ido, to ya tuntubi hukumomin da suka dace a hukumarsu mafi kusa.

Post a Comment

Previous Post Next Post