Gwamnatin Tinubu ta bawa Bankunan Nigeria iznin sayar da dalar Amurka a farashin da suka ga dama, an cire wa bankunan takunkumin da Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nigeria Godwin Emefele ya kakaba musu a harkan canjin Dalar Amurka
Abinda hakan ke nufi, yanzu darajar Dalar Amurka zata fadi kasa warwas a cikin Nigeria, saboda Dala zata yawaita, sannan farashin kayan abinci zai sauka sosai Insha Allah
Sai dai wannan mataki da Tinubu ya dauka zai bakanta ran Kasar Amurka, domin Amurka tana adawa da duk abinda zai taba darajar Kudinta
Mu yiwa Tinubu addu'ah Allah Ya kareshi daga sharrin Amerika da duk masu mugun nufi ga Nigeria