Bayan gwamnatin Kano ta rusa shataletalen gidan gwamnatin, masu ɗibar 'ganima' sun dira a wurin domin kwasar ƙarafan rodi da sauran abubuwan amfani.
Rahotannin sun bayyana ce an wayi gari ne kawai da ganin motocin rusau a kan ginin shataletalen da ke gaban gidan gwamnatin jihar.
Medialink ta rawaito cewa mutane da dama musamman a shafukan sada zumunta na ta bayyana mabambantan ra'ayoyi game da rusa ginin, wanda aka gina domin bikin cikar jihar Kano shekara 50 da kafuwa.
A baya-bayan nan dai ana sukar sabuwar gwamnatin saboda rusa wasu wuraren da gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta gina, inda ta yi zargin cewa an yi gine-ginen ne a filayen da aka mallakesu ba bisa ƙa'ida ba.
Akan butun na rusau din dai daya wasu yan kasuwar suna ganin an janyo musu asara ta milliyoyin kudi.
Tags
Labarai