Rushe ƙasaitaccen shataletale da gwamnatin Abban tayi ya janyo ka-ce-na-ce a Kano.

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta gina sabon shataletale a gaban gidan gwamnatin jihar.

Bayan da ta rushe tsohon shataletalen sakamakon dalilai na tsaro kamar yadda gwamnatin ta bayyana.

A cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnatin jihar ta tuntuɓi injiniyoyi a fannin gine-gine domin yin nazari game da ginin shataletalen kafin ta rusa shi.

A cewar sanarwar injiniyoyin sun ce ginin ba shi da inganci kuma zai iya faɗuwa tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024.

Sun ce saboda haka an gina shi da kayyaki marasa inganci, a maimakon amfani da tsantsar siminti da kyakkyawan kankare.

Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa masanan sun bai wa gwamnati shawarar cewa ginin ya yi tsawo a gina shi a gaban gidan gwamnatin jihar, saboda ya tokare babbar kofar gidan.

Inda suka  ƙara da cewa ginin na haifar wa direbobi matsaloli saboda yadda yake rufe musu ganin sauran hanyoyin da ke da mahaɗa da shataletalen.

Kan hakan ne gwamnatin jihar ta ce ya zama wajibi ta rushe ginin, domin sake fasalin shi ta yadda za ta rage tsayinsa da kuma yadda za a riƙa hango babbar ƙofar shiga gidan gwamnatin tare da kare masu ababen hawa.

Rahotonni sun ce an wayi gari da ganin motocin rusau a kan ginin shataletalen da ke gaban gidan gwamnatin jihar.


Post a Comment

Previous Post Next Post