Shugaban kasa ya umarci kai agaji ga 'yan bikin da jirgin ruwa ya kife da su a Kwara

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin kai kayan agaji da taimakon da ya kamata nan take ga mutanen da suka kuɓuta da kuma dangi da iyalan waɗanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Kwara.

Medialink ta rawaito cewa sanarwa ta foto  daga daraktan yaɗa labarai na shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye wanda yace Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi takaicin wannan hatsarin jirgin ruwa da ya kashe mutum 150 a jihar ta Kwara.

Ya kuma umarci gwamnatin jihar Kwara da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa su yi aiki tare don gano sanadi na kusa da na nesa da suka janyo aukuwar hatsarin jirgin ruwan.

Mutanen da hatsarin ya ritsa da su 'yan biki ne da ke komawa gida daga ƙauyen Egbu a cikin ƙaramar hukumar Patigi.

Cikin fasinjojin jirgin ruwan har da wani uba da ke tare da 'ya'yansa guda huɗu – kuma har zuwa yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

"Ina cike da tsananin takaici game da labarin wannan mummunan hatsari da ya haddasa asarar jama'armu a jihar Kwara" in ji Tinubu.

Shugaban ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi nazari kan matsalolin sufurin ruwa a ƙasar, nan don tabbatar da ganin ana aiki sau da ƙafa da matakan kare rayuka da ƙa'idojin aiki.

Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga gwamnati da al'ummar Kwara kan wannan hatsari

Tun da farko Mai martaba sarkin Patigi yayin zantawa da manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar ya ce gwamnan jihar Abdurraham Abdulrazaq ya kira shi, don yi masa ta'aziyya tare umartarsa ya ci gaba da magana da mutanen yankunan da lamarin ya faru, don taya su jimami da kuma gano hanyoyin da za a kaucewa sake aukuwar hatsari anan gaba.

A cewar Alhaji Ibrahim Umar Bologi, mutanen yankin suna iyakar bakin ƙoƙari wajen tsamo sauran gawawwaki da suka nutse a cikin kogi.

Ya ce daga rahotannin da ya samu, injin jirgin ne ya samu matsala lokacin da yake tafiya cikin tsakar dare.

Kafofin labaran Najeriya sun ce hatsarin ya faru ne ranar Litinin lokacin da 'yan bikin suke komawa gida bayan halartar ɗaurin aure a ƙauyen Egboti da ke cikin jihar Neja mai maƙwabtaka.

"Daga rahotannin da muka samu, kimanin mutum 300 ne a cikin jirgin ruwa," in ji Sarkin Patigi.

Ya ce garuruwa huɗu ne a yanki, kuma suna amfani da kogi a matsayin babbar hanyar sufurinsu.


Post a Comment

Previous Post Next Post