An Kaddamar Da Kwamitin Tantance Ma’aikata Sama Da Dubu 10 Da Aka Dakatar A Kano.


MEDIALINK ta rawaito cewa Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 22 domin tantance ma’aikata sama da dubu 10 da aka dakatar, wadanda aka dauka aiki a karshen wa’adin gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Baffa Bichi, ya ce kwamitin zai tabbatar da ko anbi ka’ida wajen daukar ma’aikata.

Kwamitin zai yi aiki bisa jagorancin shugaban hukumar daukar ma’aikata, Alhaji Umar Shehu Minjibir, kuma an baiwa kwamitin wa’adin makonni biyu ya kammala aikinsa.
A martanin da ya mayar, Minjibir ya yi alkawarin cewa mambobin kwamitin za su yi iya kokarinsu don ganin sun kammala aikin a kan lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post