Gwamnatin Katsina Ta Amince Da Sayo Karin Motocin Sufuri 40 Domin Saukaka Matsalar Sufuri


A kokarin da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamnan Umaru Dikko Radda take na ganin ta saukaka wa al’ummar jihar.

MEDIALINK ta rawaito Gwamnan jihar ya amince da a fitar da kudi Naira miliyan 600 domin siyo karin motocin sufuri guda 40 ga hukumar sufuri ta KTSTA, ta yadda al’ummar jihar Katsina za su samu saukin tafiyar da lamurransu na yau da kullum.
Matakin ya biyo bayan zaman majalisar zartarwa na jihar da ya gudanar a ranar Larabar  16th ga Agusta, 2023 a gidan gwamnatin jihar, Katsina.

Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na jihar Dr Sani Magaji Ingawa ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwar.
Kwamishinan ya ce Gwamna ya umurci cewa za a yi amfani da motocin wajen sufurin ciki da wajen jihar kamar yadda hukumar sufurin KTSTA take gudanar da ayyukanta.

Dr.Magaji Ingawa ya ce Gwamna ya kuma ce za a yi amfani da wani kaso na motocin domin daukar daliban makarantun firamare da na sakandare da ma na makarantun gaba da sakandare da ke jihar, duk don a saukaka musu wajen zuwa makaratunsu cikin lokaci.

Gwamnatin jihar ta sanar da cewa ba za a tsawwala farashin hawa wadannan motoci ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post