Gwamnatin Jihar Katsina zata Fitar Da Biliyan N7.8bn Domin Sayen Kayan Aikin Tsaro.

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya amince da fitar da zunzurutun kudi har kusan naira biliyan takwas da za a yi amfani da su don sawo kayayyakin aikin samar da tsaro na zamani don inganta tsaron al’ummar jihar Katsina.

MediaLink ta rawaito kwamishinan lamuran da suka shafi tsaron ciki gida na jihar Katsina Dr Nasir Mu’azu Danmusa, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gidan Gwamnatin jihar bayan kammala zaman majalisar zartarwa na jihar wanda gwamma Radda ya jagoranta.
Gwamnatin za ta kashe N7,813,423,560.83 domin sayen sabbin kayayyakin aikin tsaro na zamani da za a raba wa jami’an tsaron dake aiki a jihar Katsina don ganin Gwamnatin ta inganta rayuwar al’ummar wajen samar da tsaro da zaman lafiya.
Idan za a iya tunawa dai jihar Katsina ta dade tana fama da harin yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, wanda hakan ya ke haifar da dardar a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post