Shugaban karamar Hukumar Kumbotso Hon. Hassan Garban Kauye Farawa ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Alhaji Ibirahim Yusuf Mai Kalwa da mutanen yankin bisa rasuwar Hakimin Mai Kalwa, wanda ya rasu yana da shekaru 85 a duniya. Bayan fama da rashin lafiya na dogon lokaci. Ya bar mata uku da ‘ya’ya 10.
“Ina ciki damuwa alokacin da na samu labarin rasuwarsa, kuma ba zan iya bayyana irin da muwar da al’umma da iyalan Marigayi Alhaji Ibirahim Yusuf suke ciki ba, ba marigayi Mai Kalwa kadai ne. shugaba mai daraja amma kuma ginshikin karfin al'ummar mu tare gudummuwar da ya bayar wajen ci gaban karamar hukumar Kumbotso za a rika tunawa da shi har abada abadin.
Tarihin marigayi Alhaji Yusuf Mai Kalwa zai kasance a cikin zukatanmu har abada, kuma tasirinsa ga al'ummarmu zai ci gaba da mana jagora a cikin ayyukanmu. Muna fatan cewa, iyalin shi za su sami kwanciyar hankali a cikin abubuwan tunawa.
“Ina mika ta’aziyyata ga al’ummar Na’ibawa Mai Kalwa da iyalan Marigayi Ibirahim a cikin wannan mawuyacin lokaci, rasuwar hakimin ya haifar da gibi a cikin al’ummarmu wanda zai yi wuyar cikawa, ya kasance shugaba nagari, kuma za a yi kewar matuka”.
Garban Kauye ya ce, “Ya samu damar yin aiki tare da Marigayi Mai Kalwa wajen gudanar da ayyuka daban-daban na al’umma, kuma sadaukarwar da ya yi da jajircewarsa na da ban sha’awa sosai, ya kasance mai son al’umma, kuma abin da ya gadar zai ci gaba da wanzuwa cikin kyawawan sauye-sauyen da ya kawo Kuma ina rokon Allah ya sa Aljannatul Firdausi ta zama gidansa na karshe".
Sanarwa daga Shazali Sale Farawa,Mai taimakawa shugaban karamar hukumar akan yada labarai.
Tags
Ta'aziya