An bukaci kwamishinwn ayyuka na Jihar Kano Engr Marwan Ahmed da yayi biyayya ga tanade-tanaden doka ya bada bayanan da kungiyar War against injustice ta nema kafin kwana 7.
Kungiyar nan mai zaman kanta wacce take fafutakar yaki da rashin adalci, Kare Hakkin Dan Adam da bibiya a kan shugabanci nagari me suna War Against Injustice ta bukaci kwaminshinan ma'aikatar aiyuka da raya kasa na jihar Kano Engr. Marwan Ahmad yayi biyayya ga dokar yancin samun bayanai ta 2011 ya bawa Kungiyar bayanan da ta nema karkashin dokar yancin samun bayanai a ranar 27 ga watan 7 2023.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata takardar tuni a kan bayanan da Kungiyar ta aike masa yau mai dauke da sahannun babban direktan Kungiyar Comr. Umar Ibrahim Umar.
Idan za'a tuna a ranar 27-7-2023 ne Kungiyar ta bukaci kwaminshinan ma'aikatar ya bata cikakken bayanai, guraren da kalar aiyukan mazabu na yan majalisar dokokin Kano 40 da aka aikewa ma'aikatar tayi tun daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Tags
Labarai.