Shugaban majalisar dokokin jihar Kano Rt.Hon.Jibiril Isma'il Falgore yace majalisa zata gayyaci Auwal Salisu domin girma shi tare da bashi gudun mawa daga cikin albashin kowanne Dan majalisa domin ya bawa wanna yaro Mai kananun shekaru kuma yake da imanin Mai da wadannan makudan kudade duk kuwa da cewa su talakawa ne Dan sahun Mai suna Auwal Salisu ya dauki mutane biyu ne idan bayan ya sauke su yaga sun manta da wani buhu idan ya bude yaga kudi ne sai ya koma idan ya aje su amma bai same su ba.
Inda ya Kai kudin ga mahaifan shi Suma suka Goya Mai baya wajen aje kudin da jiran ta idan zaa nemi kudin sai gashi mahaifiyar shi taji a gidan radio Arewa ana cigiyar kudin idan sukai gidan radio domin Maidawa Mai kudin kayan shi.
Dan majalisar da ya kawo kudirin na gaggawa Hon Salisu Muhammad Doguwa ya bukaci majalisar data nemi gwamanatin kano ta taimakawa yaro da iyayen shi bisa irin wannan gaskiya da ya nuna a wannan lokacin da ake cikin na matsin rayuwa kuma ta ayyana shi amatsayin gwarzon shekara ta 2023.