Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago sun cimma matsaya kan dakatar da yajin aikin da kungiyar ta shirya yi a fadin kasar bayan wata ganawar sirri da suka yi a fadar shugaban kasa ta Villa Abuja.
MediaLink ta rawaito cewa shugaban kungiyar Æ™wadago ta NLC, Joe Ajaero ya ce N25,000 da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar a jawabin cikar Nigeria shekaru 63 da samun ‘yancin kai zai fara aiki ne ga dukkanin ma’aikata mai makon kananan ma’aikata da aka fada a baya, Kuma ya kara Naira 10,000 ya koma Naira 35,000.
Haka zalika, gwamnatin tarayya ta amince za ta cire kaso 7.5% na haraji, VAT da ake biyawa man dizal domin tabbatar da rage farashin kayayyakin da ake amfani da su, wanda dama da shi ne kamfanoni suke amfani wajen samar da wutar lantarki a masana’antu da ofisoshi.
Inda Shugabancin Kungiyar Kwadago zai gana da gamayyar kungiyoyin ma’aikata domin sanar da matakin dakatar da yajin aikin da aka shirya gudanarwa a fadin kasar baki daya da aka tsara farawa daga tsakar daren Talata 3 ga watan Oktoba.
A halin da ake ciki, Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago za su ci gaba da tattaunawa a ranar Litinin don kara samun daidaito kan batutuwan da suka shafi batun cire tallafin man fetur.
Tags
Labarai.