A jawabinsa tunda fari, ya bayyana cewa zasu mayar da hankali kan janyo yan jarida ajikin su domin samun dangantaka mai dorewa, musamman wajen bayar da rohotannin dasuka shafi tsaro.
Lagbaja yace a shirye suke wajen baiwa yan jaridu kariya da kuma taimaka musu wajen samun sahihancin labari.
Medialink ta rawaito cewa Akarshe yaja hankalin yan jarida wajen wallafawa tare da bayar da sahihin labari musamman wanda yashafi tsaro.
Taken tattaunawar na bana shi ne, Habbaka hadin gwiwa tsakanin farar hula da soji, da kuma mayar da hankali kan dangantakar sojojin Nijeriya da kafofin yada labarai..
Tags
Labarai