Dan Majalisa dokokin Jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Bunkure Hon. Hafizu Gambo, yace sunyi kudirori tare da dokoki da suka ciyar da al'umar Jihar Kano da karamar hukumar Bunkure gaba a shekara daya da zuwan gwamanatin su ta N.N.P.P
Wanda ya Kara da cewa majalisa ta goma tayi abin azu a gani ta yadda suka saka bukatun al'umar Kano dana kananan hukumomin da suka zabo su Sama da komai.
Hon. Hafizu Gambo ya kuma ce sun gabatar da kudirori da suka shafi hanyoyi da bangaren lafiya da ilimi da sauran abinda al'umar da suka zabe shi a kai duk kuwa da cewa yanzu suka fara ta hanyar biya-biya idan sunyi kudiri ta yadda har sai gwamanatin Engr. Abba Kabir Yusuf ta gudanar da bukatun al'umar su.
Hon.Gambo yace a zuwan shi ya bada tallafi ga mata da matasa domin ingata rayuwar su tare da dogaro da kai a shekara guda da yayi a majalisar dokokin Jihar Kano.